Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya sake caccakar ’yan majalisar tarayya da jihohi, yana bayyana cewa halayensu na cin hanci da rashawa sun zarce na da.
A cewarsa, tsarin da ake kira ayyukan mazabu ya zama wata hanya ta sace kudin jama’a a bainar jama’a, abin da ya kwatanta da “sata da rana tsaka ba tare da kunya ba.”
Obasanjo ya yi wannan furuci ne yayin wani taro a Abuja inda ya yi bayani game da littafinsa mai taken
“Najeriya jiya da gobe: Nazari kan tarihin Najeriya da makomarta.”
Ya tuna irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin yana shugaba, musamman game da yadda ’yan majalisa suka yi yunkurin hana kafa hukumar EFCC saboda tsoron kada su shiga gidan yari bayan wa’adinsu.
Ya bayyana cewa sai da aka yi shekara ɗaya da rabi ana kai ruwa rana kafin majalisar ta amince da dokar kafa EFCC, kuma hakan ya nuna yadda wasu daga cikinsu ke tsoron shari’a idan suka amince da dokar yadda aka kawo musu.
A cewar tsohon shugaban kasar, abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne yadda ’yan majalisa suka wuce iyakarsu wajen ƙayyade albashi da alawus-alawus, suna watsi da kundin tsarin mulki da ya bai wa hukumar RMAFC wannan iko.
Obasanjo ya ce hakan ya jawo suka fi ’yan majalisun wasu ƙasashen da suka ci gaba wajen samun kuɗaɗen alawus da albashi.
Ya kuma bayyana cewa lokacin mulkinsa ya ƙi amincewa da wasu kuɗaɗe da majalisar ta ware don kashewa kan abubuwan da ba su da amfani, abin da ya jawo masa barazanar tsigewa daga majalisar.
A cewarsa, ayyukan mazabu wata hanya ce ta wawure kuɗin jama’a ba tare da amincewar bangaren zartarwa ba, wanda hakan ya lalata tsarin kasafin kuɗi ya kuma jefa Najeriya cikin gibin tattalin arziki.
Obasanjo ya ƙara da cewa halin da ake ciki a yanzu ya fi muni, musamman daga lokacin gwamnatin baya, inda majalisar ta fara yin hakan a fili ba tare da wani kunya ba.
Ya bayyana cewa idan shugaban ƙasa ya kasa taka musu burki, to shi ma ya zama abokin laifin.
A wani bangare na jawabin nasa, Obasanjo ya jaddada cewa a lokacin da yake shugaba daga 1999 zuwa 2007, gwamnatinsa ta yi iyakar ƙoƙarinta wajen kyautata tattalin arzikin Najeriya, inda ya sauka daga mulki ƙasar tana da rarar kudi, ba kamar yadda ya same ta cikin bashi ba.
atakaice:
Olusegun Obasanjo ya sake bayyana rashin gamsuwarsa da ayyukan ’yan majalisar Najeriya, yana zarginsu da satar kuɗin jama’a ta hanyar ayyukan mazabu. Ya yi nuni da cewa tsarin ya lalata kasafin kudi kuma ya tsananta cin hanci. Obasanjo ya yi kira da a duba matsalar domin ta zama barazana ga ci gaban ƙasar.
👉 Menene ra’ayinka game da wannan magana ta Obasanjo? Ka bayyana tunaninka a ƙasa.