Atiku Abubakar ya Gargaɗi Gwamnatin Tinubu Kan Danne ‘Yan Adawa Kafin Zaben 2027

Atiku Abubakar yana gargaɗi ga gwamnatin Bola Tinubu kan danne ‘yan adawa kafin zaben 2027.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan matakan da yake zargin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke dauka don murkushe ‘yan hamayya. A cewarsa, wadannan matakan suna iya haifar da rikici da kara rarraba kasar, musamman a lokacin da ake shirin tunkarar zaben shekarar 2027.

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, ya yi wannan gargadin ne bayan gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda shi ma jagora ne a jam’iyyar hadaka ta ADC. Haka kuma, Atiku ya nuna damuwa kan hare-haren da ake kaiwa kan wasu mambobin jam’iyyun adawa, yana mai cewa hakan na nuna shirin da ake yi na raunana su domin su kasa shiga gasar siyasa.

Mai magana da yawun Atiku, AbdurRashid Shehu Sharada, ya ce alamu sun nuna cewa gwamnatin yanzu tana yin duk mai yiwuwa don ganin babu wata jam’iyyar adawa da za ta iya tsaya wa takara mai karfi a zaben mai zuwa. Ya ce, “Yanzu haka, jam’iyyun adawa suna cikin rikice-rikice da rashin jituwa saboda ana amfani da hanyoyin siyasa da kuma bangar siyasa domin raba kawunansu.”

Sharada ya kara da cewa an hana taron dattawan jihar Katsina da aka shirya don tattauna matsalar tsaro ta jihar, inda aka turo wasu ‘yan bangar siyasa don hana zaman ya gudana cikin kwanciyar hankali. Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda aka tura wasu mutane su tayar da zaune tsaye a taron jam’iyyar ADC da El-Rufai ya jagoranta a gaban jami’an tsaro, amma duk da haka babu wanda aka kama. Sai ma kuma ‘yan sanda suka yi wa El-Rufai da wasu shugabannin adawa tambayoyi, abin da Sharada ya kira babban abin kunya.

Duk da wadannan zarge-zarge, mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, Abdul’Aziz Abdul’Aziz, ya musanta su baki daya. A cewarsa, ba wani jami’in gwamnati ko hukumar tsaro da za ta cutar da wani dan kasa ba tare da dalili mai karfi ba. Ya ce, “Gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa Malam Nasir El-Rufai ta shafi kalamansa da ayyukan wasu daga cikin magoya bayansa, ciki har da zargin cewa ana yawo da makamai a taruka. Wannan doka ce kawai ke aiki.”

Abdul’Aziz ya kara da cewa harin da aka kai tsohon ministan shari’a a Kebbi da kuma taron da aka gudanar a Katsina ba su da alaka da gwamnatin tarayya, yana mai bayyana su a matsayin al’amuran siyasa da hukumomin tsaro za su ci gaba da bincikawa.

Masana harkokin siyasa sun yi kira ga gwamnati da jam’iyyun adawa da su yi taka-tsantsan da kalamansu da matakan da suke dauka. Sun ce idan aka ci gaba da zafafa siyasa ba tare da la’akari da al’umma ba, hakan na iya haifar da rikicin da zai shafi makomar kasar gaba daya.

Wannan rikici na kara bayyana yadda siyasar Najeriya ke kara daukar zafi, yayin da kowanne bangare ke neman karfi kafin babban zaben 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *